Iri | Mutuwa |
---|---|
Mutuwar Vincent van Gogh, mai zane ɗan kasar Holand, ya faru ne da sanyin safiyar ranar 29 ga watan Yulin 1890, a cikin ɗakinsa a Auberge Ravoux a ƙauyen Auvers-sur-Oise a arewacin Faransa. Kwanaki biyu kafin nan, Van Gogh ya harbe kansa ko kuma da gangan wani ya harbe shi. Yayin da takardar shaidar mutuwarsa ta bayyana cewa ya mutu ne a dalilin cewa ya kashe kansa, akalla wasu masu rubuta tarihin rayuwa su biyu sun kalubalanci hakan, inda suka ce mai yiwuwa wani ne ya harbe shi da gangan.
© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search